Wani matashi mai suna Chisom Eze ya kashe dan uwansa Henry dan shekaru 19 da haihuwa, akan kwalbar Lemo, hakan ya faru ne a anguwar Johnson dake yankin Alaba na Jihar Legas.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Chisom ya bar Lemon ya fita domin yin wani uzurinsa, a yayin da ya dawo sai ya tarar dan uwan nasa na shanye Lemon.
Cikin fushi ya dauki wuka ya dabawa dan uwan nasa a wuya. https://dimokuradiyya.com.ng/yan-sanda-sun-kashe-masu-garkuwa-da-mutane-har-mutum-8-a-jihar-taraba-2/
‘Yar uwarsu da ta ganewa idonta faruwar lamarin, nan take t kurma ihun neman dauki ga makota, kuma nan take aka kawo agaji wajen kama Chisom.
Sai dai kafin a kai Henry asibiti domin ceto rayuwarsa yace ga garinku nan.
Da aka tuntubi kakakin hukumar’yan sanda na jihar Bala Elkana yace “Chisom ya dabawa kaninsa wuka a wuya, kuma yanzu yana hannunmu, ana cigaba da bincike”.