By Ishaq Dabai
Rikici ya barke a kan babbar hanyar Afikpo-Abakaliki a jihar Ebonyi sakamakon kisan wasu matasa uku da wata mota tayi a yankin.
Wata majiya data zanta da manema labarai a kewayen Unguwar Akpoha dake karamar hukumar Afikpo ta Arewa ta jihar ta nuna alhinin ta game da wannan ci gaba sannan ta shawarci matafiya dasu koma baya don kaucewa munin lamarin.
“Ba mu yi farin ciki da wannan ci gaban ba. Wata babbar mota ta kashe matasan mu uku sannan ta jefar da gawarwakin su cikin daji kuma muna zanga zanga akan hakan.
“Zan bamu shawara mu koma baya bamu da farin ciki ko kaɗan ta yaya direban motar zai kashe matasan mu ya boye gawarwakin su. ”
A halin yanzu, babbar hanyar Afikpo zuwa Abakaliki dake gefen Akpoha da alama matafiya baza su iya wucewa ba yayin da motoci ke tsayawa a kan babbar hanyar yayin da wasu ke juyawa da baya don gujewa kasancewa a tsakiyar tashin hankalin.
Lokacin da da jaridar Vanguard ta tuntubi hukumomin da abin ya shafa cikin harda Gwamnati da jami’an tsaro a jihar game daci gaban, sun ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a shawo kan lamarin.
Sannan gwamnan jihar David Umahi yace”Taimako zai zo nan da nan batare da bata lokaciba”in jishi
A halin da ake ciki, Kwamishinan ‘yan sanda, CP Garba yayi bayanin cewa“ sakamakon mummunan hatsarin mota ne inda wani direban okada da fasinja suka gamu da ajalinsu ”
Rahotanni sun bayyana cewa Shugaban Majalisar kuma Mai Gudanarwa yana kan wannan lamarin kuma sun kawar da matsalar hanyar.
Comments 1