By Ishaq Dabai
Hukumomin shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen kungiyar ECOWAS sun kuduri aniyar dakatar da kadarorin tare da sanya takunkumin tafiye tafiye kan mulkin soja a kasar Guinea.
A cikin sanarwar da aka fitar a karshen Babban Taron na ranar Alhamis da aka gudanar a Ghana, shugabannin ECOWAS sun kuma bayar da wa’adin watanni shida don komawa kan mulkin demokradiyya ga shugabannin juyin mulkin.
Babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Laolu Akande, shine ya bayyana hakan a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Babban taron ECOWAS na musamman,kungiyar ECOWAS ta dage kan hanzarta mika mulki zuwa mulkin farar hula a Guinea’.
Ku tuna cewa a taron karshe na shugabannin ECOWAS wanda aka gudanar a ranar 8 ga Satumba, wanda Osinbajo ya wakilta Najeriya ta yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Guinea, inda ta yi kira da a saki Shugaba Alpha Conde ba tare da wani sharadi ba, da kuma tsauraran matakai kan mulkin sojan Guinea.
Da yake jawabi a taron Accra, Osinbajo ya sake jaddada matsayin Najeriya ta hanyar yin kira da a saki Shugaba Condé ba tare da wani sharadi ba da kuma kara matsa lamba ga shugabannin sojojin kasar da su mayar da kasar kan mulkin dimokuradiyya.
Game da sabunta halin da ake ciki a Mali, Mataimakin Shugaban ya yabawa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan “saboda ci gaba da jajircewarsa da hulɗa da masu ruwa da tsaki a Mali.”
“Don tabbatar da an dakatar da Guinea daga dukkan hukumomin da ke karkashin ECOWAS har zuwa lokacin da za’a maido da tsarin mulkin farar hula don tabbatar da gudanar anyi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu cikin watanni shida don maido da tsarin mulki a Jamhuriyar Guinea,sannan mun hana tafiye tafiye kan membobin CNRD na gwamnatin sojan Guinea da membobin danginsu da kuma dakatar da kadarorinsu na kuɗi.”
Baya ga mataimakin shugaban kasa, zaman ya kuma samu halartar shugabanni takwas da ministocin harkokin waje 4 da ke wakiltar shugabannin kasashe, tsohon shugaban Najeriya kuma mai shiga tsakani na ECOWAS kan Mali,Dakta Goodluck Jonathan, shugaban hukumar ECOWAS, Jean-Claude Kassi Brou, Wakili na musamman Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya a Yammacin Afirka, da sauransu.