Taron da shugabannin kasashen yammacin Afirka membobi a kungiyar Cedeao ko kuma ECOWAS da aka fi sani sun gudanar da taro ta bidiyo a jiya Laraba, inda suka sanar da sanya takunkumi da dama ga kasar Guinea Conakry sakamakon juyin mulkin da aka yi wa Alpha Conde.
Ministan Harkokin wajen Burkina Faso Alpha Barry, ya ce daya daga cikin matakan da taron ya dauka sun hada da dakatar da Guinea daga kasancewarta memba a kungiyar ta ECOWAS.
A lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron a jiya, shugaban riko na kungiyar ta ECOWAS wato shugaban Ghana Nana Akufo-Ado, ya bayyana juyin mulkin da cewa, ya saba wa dokokin kare dimokuradiyya da kyakkyawan jagoranci da kungiyar ta shimfida.
Har wala yau a wani banger na taron, kungiyar ta kuma bukaci sojoji su gaggauta sakin hambararren shugaba Farfesa Alpha Conde, tare da yanke shawarar tura tawaga ta musamman zuwa birnin Conakry don ganawa da sojojin da suka yi wannan juyin mulki a yau Alhamis.