Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS a ranar Litinin din nan ta yi alkawarin sassauta takunkumin tattalin arziki da na kudi a kan kasar Mali.
Shugaban kungiyar ta ECOWAS Jean-Claude Kassi Brou ne ya bayyana hakan a wajen rufe taron manema labarai na taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 61 a birnin Accra.
A cewar Brou, hukumomin kasar Mali sun dauki matakai wajen zartar da yarjejeniyar zabe da kuma kafa tsarin sa ido kan mika mulki.
Ya ce hukumomi sun kuma dauki matakin shirya sabon kundin tsarin mulkin kasar.
Ya ce za a kawo karshen mika mulki a Mali a watan Maris din shekarar 2024 a cikin tsarin mika mulki na watanni 24.
Brou ya ce ECOWAS ta yanke shawarar dage duk wani takunkumin tattalin arziki da na kudi da aka sanya mata a ranar 9 ga watan Janairu.
“Wannan yana nufin, da gaske, rufe kan iyaka, daskarewar kadarorin kudi.
“An cire waannan takunkumin,” in ji shi,
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, ya kara da cewa jakadun kasashe mambobin ECOWAS a Mali za su koma Mali.
“Duk da haka, yayin da ake bukatar a sanya ido kan tsarin, shugabannin kasashe sun yanke shawarar ci gaba da sanya takunkumi na kowane mutum da kuma ci gaba da dakatar da Mali daga sassan cibiyoyin ECOWAS,” in ji shi. (NAN)