Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya bukaci mazauna jihar da su marawa kudirin gwamnatin sa na ci gaba da sauye-sauyen hukumomi a sassa daban-daban na gwamnati, ta yadda za a kyautata rayuwar kowa.
Gwamnan, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a birnin Benin, kan ci gaban da jihar Edo ta samu kawo yanzu a daidai lokacin da ake cika shekaru 31 da kafa ta a shekarar 1991, ya ce jihar ta samu sauyi sosai a shekaru 31 da yawan al’ummarta ya rubanya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan Sanda Sun Cafke Masu Kaiwa ‘Yan Bindiga Bayanan Sirri
Ya kara da cewa: “A shekaru 31 da kafuwar jihar Edo ta canza Yawan jama’a ya ninka fiye da ninki biyu kuma cibiyoyin da aka gada shekaru 31 da suka gabata sun tabarbare sosai.”
“Daya daga cikin abubuwan da muke yi a matsayinmu na gwamnati shi ne sake gina cibiyoyinmu don karfafa ingancin ma’aikatan gwamnati, ingancin ilimi da ingancin ayyukan kiwon lafiya, da kuma samar da mafi inganci a kasar nan.”
“Kalubalen mu shi ne ta yaya za mu inganta ma’auni na cibiyoyinmu da mayar da su kan matsayin da muka saba da su kuma za a iya wuce irin wadannan matakan? Ina kira ga al’ummar Jihar Edo da su ci gaba da zama masu kwarin guiwa, domin a halin yanzu birnin Benin ya zama wata matattarar zuba jari.”
“Muna aiki ba tare da gajiyawa ba a matsayinmu na gwamnati, samar da yanayin zaman lafiya da kasuwanci tare da jan hankalin masu zuba jari da kuma mayar da jihar ta zama cibiyar zuba jari.”
“Tuni dai jihar ta cika da cunkoson ababen hawa domin da yawa suna shigowa jihar. Wani abu mai kyau yana faruwa a jihar Edo wanda kowa ke son kasancewa cikinsa.”
A wani labarin kuma Yajin Aiki Ya Shiga Kwanaki Na 196, Yau Ne ASUU Zata Yanke Shawara
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka fara wani taro na Majalisar Zartaswa ta Kungiyar Malaman Jami’o’i da ke yajin aiki a Abuja, kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito.
Ana sa ran kungiyar za ta yanke shawara ta karshe kan ko za ta ci gaba da ayyukanta na masana’antu da suka shiga kwanaki na 196 a ranar Litinin (yau) a taron da za ta yi a hedikwatarta ta kasa da ke Jami’ar Abuja.