By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan Sanda ta jihar Edo tare da hadin guywa da kungiyar Vigilante sun kama mutane biyar masu garkuwa da kuma yan fashi da makami a ranar Asabar a kan babban titin Benin zuwa Legas, inda kuma ‘yan Sanda suka cafke karin wasu masu garkuwa mutum biyu.
Rahotonni sun bayyana cewa wadanda ake zargin sun biyo a yarin masu kai gawa akan babura daga Legas zuwa Jihar Imo a kusa da kogin Ute dake kan babban hanyar Benin zuwa Legas a ranar Juma’a inda kuma sukayi garkuwa da mutane uku dake kan baburan.
Rundunar ‘yan sanda data Vigilante sun hada kai inda suka shiga cikin dajin suka kubutar da wadanda aka kama tare da kama masu laifi guda biyu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Bello Kangtons ya tabbata da faruwar hadarin inda yace tare da hadin guywa da kungiyar Vigilante sun kama wanda suke zargin.
Sannan ya kara da cewa sun kama mutane biyu Mohammed Ishaku mai shekaru 25,da kuma Mubarak Wada mai shekaru 26, da sauran wadanda suka kubuta da kuma wanda harsashi ya samu.
Ya kara da cewa mutane ukun da aka kubutar da mutane biyun da suka kama sun kaisu asibitin dan basu agajin gaggawa, sannan yace sun sami bindiga kirar gida guda uku da harsasai guda biyu da kuma adduna guda biyu wanda suka kwace daga waje masu laifin.