EFCC

EFCC Sun Gurfanar Da Maina Bisa Zargin Aikata Laifuka 12

An tsaurara jami’an tsaro a babban kotun gwamnatin tarayya dake Abuja a yau Juma’a, a yayin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya wato EFCC suka gurfanar da Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar Fansho.

Rahotanni sun bayyana cewa; har wala yau ma an gurfanar da yaron Maina din wato Faisal a gaban kotun bisa wadansu zarge-zarge na daban.

Kotu ta 6, dake gini na biyu, inda mai shari’a Okon Abang zai jagoranta, ta cika da gamayyar Lauyoyi.

Maina da dansa Faisal suna sanye da fararen kaya da kuma hula ‘Blue.’

Ya zuwa hada rahoton nan da misalin karfe 10:30 na safe, ba a kai ga kiran shari’ar na su ba.

Sai dai hukumar EFCC din sun gurfanar da Maina ne bisa zarge-zarge 12 wanda ya hada da ta’ammuli da kudi ba bisa ka’ida ba, da kuma amfani da wadansu asusun banki da kuma almundahana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *