By Ishaq Dabai
Kwamandan shiyyar Legas na hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta cafke wani mutum mai suna Abraham Adeniji bisa zarginsa da samun kayayyaki ta hanyar yaudara da karkatar da kudi zuwa 82, 803,550.00.
An cafke shi ne bayan wata takarda da Hukumar ta karba daga Gao Shu Quin, dan kasar China.
Mai shigar da karar ta yi zargin cewa ta hadu da wanda ake zargi ne a wani lokaci a shekarar 2017 yayin da take gudanar da kasuwancin ta na halal.
Ta ci gaba da zargin cewa wanda ake zargin ya yaudare ta ta ba shi kwantena na kayan yadi, tana ganin zai turo kudin da aka samu idan aka sayar da kayan yadi.
Sai dai wanda ake zargin ya karkatar da kudin da ya samu don amfanin kansa bayan ya sayar da kayan.
Nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu da zaran an kammala bincike, a cewar wata sanarwa da kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya rabawa manema labarai a daren ranar Litinin.