Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati a Najeriya, EFCC ta gurfanar da Aisha Wakil wadda aka fi sani da ‘Mama Boko Haram’ da wasu mutum biyu kan zargin almundahanar miliyan 111 a gaban kotu.
Hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ta gurfanar da Aisha Wakil tare da Tahir Sa’idu da kuma Prince Lawal Shoyode a gaban mai shari’a Aisha Kumalia da ke Babbar Kotun jihar Borno kan zarge-zarge biyar.