Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa EFCC shiyar Port Harcourt ta ce, jami’an ta sun kama Mutane 15 da ta ke zargin masu damfara ta yanar gizo ne.
Hukumar ta ce, ta yi nasaran kama wadanda ake zagin ne, a wani samame da ta kai a jiya Talata, 31 ga watan Agustan shekarar 2021, a maboyansu daban-daban dake garin Aba a jihar Abia.
Jami’in Hulda da kafafen yada labarai na hukumar EFCC Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa da ya fitar, Kuma ya bai wa manema labarai a garin Port Harcourt babban birnin jihar Rivers.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan majalissar dokokin Anambra guda 6 sun koma APC
Sanarwar ta ce, ” An kama wadanda ake zargin ne a Gini mai lamba 214b, dake kan hanyar Aba zuwa Owerri, da Cherubim Owo Osisioma, da kuma wurin aje motoci na Nwanyu, dake yankin Umuode Osisioma na garin Aba a jihar Abia, bayan wasu bayanan sirri da hukumar ta samu kan wadanda ake zargin da damfara ta yanar gizo”
Kazalika sanarwar ta bayyana sunayen wadanda ake zargin kamar haka: Ezekiel Udo, Anyanwu Odinakachi, Emeka Agu, Lawrence Chinaza Michael, Ifeanyi Okorie, Nestor Akobunu, Frank Ogu, Ezekiel Samuel Uche, Inegbu Onyema Uche, Azukaogi Ogiegbe, Okoro Uchechukwu, Victor Ehiudo, John Chiemela, Lucky Nwoko da kuma Ugochukwu Emmanuel Okafor.
“An kama sune tare da Motoci guda Uku, da suka hadar da: Lexus RX350, da GLK Benz SUV, da kuma Lexus ES33O SUV” inji sanarwar.
” Sauran kayayakin sun hada da; wayoyin hannu daban-daban guda 43, da kuma wayoyin Tangaraho guda 7, Na’urar daukar Hoto na zamani guda 2, Laptop guda 8, da kuma agogunan hannu kirar iPhone guda 3.” a cewar sanarwar.
Comments 1