Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) na shiyyar Ilorin sun kama mutane 16 bisa zarginsu da aikata laifuka ta yanar gizo da kuma mallakar makudan kudade ba bisa ka’ida ba a Ilorin, jihar Kwara. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren, ya fitar a ranar Juma’a, ta ce an kama su ne a ranar Alhamis, biyo bayan sahihan bayanan sirri da hukumar ta gudanar.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: NNPP Ta Sha Alwashin Karbe Mulki Daga Hannun Jam’iyyar PDP A Jihar Enugu
Sanarwar ta ce, kayayyakin da aka kwato daga wajensu sun hada da wasu manyan motoci guda takwas, wayoyi da kwamfutoci.
Wadanda ake zargin da suka hada da ‘yan uwa biyu Ahmed Ismail da Toheeb Ismail, su ne, Suleiman Abduqudrib Salati, Nurudeen Ibrahim, Boluwasefe Oyinloye, Bashir Azeez, Abduquodri Ibrahim, Raji Roqeeb, Tobiloba Raihan, Busari Mohammed
Sauran sun hada da, Olaoye Kolade, Bello Muhammed, Onime Bright, Adebayo Bolaji, Abdulqudus Zakariya da Adeleke Hassan.
Sanarwar ta kara da cewa ” nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.”
A WANI LABARIN KUMA: Jami’ar Sufurin Jiragen Sama Zata Fara Rajistar Daukar Dalibai – Sirika
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika a ranar Juma’a ya sanar da cewa Jami’ar Sufurin Jiragen Sama ta Afirka da Aerospace za ta fara rajistar zangon karatu na 2022/2023 daga ranar 26 ga watan Satumba zuwa 18 ga watan Nuwamba 2022.
Ya bayyana hakan ne a ci gaba da tattaunawa da kafafen yada labarai kan jami’ar sufurin jiragen sama.