Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa tattalin arzikin kasar zakon kasa wato EFCC shiyar Ilorin sun cafke mutane 30 da ake zargi masu damfara ta yanar gizo ne, a wani samame da suka kai jami’ar jihar Kwara, KWASU dake garinMalete.
An cafke wadanda ake zargin ne bayan bayanan sirri da aka samu kan zarginsu da hannu cikin ayyukan damfara ta intanet.
Wasu daga cikin bayanan sirri sun nuna cewa, wadanda ake zargi da damfarar yanar gizo, suna aiki a cibiyoyin karatun da ke kewayen birnin Ilorin, don damfarar wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, saboda samun kudin da suke kaushewa.
Rahotanni sun nuna cewa, Jami’an Hukumar EFCC sun kai samamen ne makarantar ne a ranar 19 ga Satumba shekarar 2021, inda sukayi nasarar kama da dama daga cikinsu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Mutane 9 sun rasa rayukan su sanadiyar hadarin mota a Edo
Wasu daga cikin abubuwan da aka samu a hannun wadanda ake zargin sun hada da; Motoci guda shida masu ban mamaki, kwamfyutocin tafi -da -gidanka masu dumbin yawa, wayoyin hannu da dai sauran su.
Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya manta sabo da zaran an kammala gudanar da bincike.
A wani labarin Kuma na daban
Jahar Edo ta tabbatar da mutuwar karin mutane biyar, wadanda ba’a yiwa allurar rigakafin COVID-19, inda Gwamnatin ke cigaba da kira ga yan kasar, dasu fito domin karbar rigakafi, domin su kasance cikin koshin lafiya.
Jami’in Kula da cutar Covid-19 na Jaha Dr Andrew Obi ya bayyana haka, bayan taro ta yanar gizo da Kwamitin bada agajin gaggawa na cutar, wanda Gwamnan Jahar Mr Godwin Obaseki ya jagoranta.
Obi yace uku daga cikin wadanda suka rasu an samu rahoton su ne daga Asibitin Stella Obasanjo, a yayinda sauran mutum 2 aka same su a Asibitin kwararru na Irrua, inda ya kara dacewa, an samu karancin mutuwar mutane a kashi na uku na cutar a Jahar da mutane 64.
Manajan wanda ya jaddada bukatar dake akwai na mazauna Jahar da suje su karbi maganin rigakafin cutar, yace Gwamnatin Jahar ta yiwa mutane dubu 82,849 rigakafi a fadin jahar a kashi na biyu na rigakafin.
Ya kara dacewa, Jahar a ranar Talata 21 ga watan Satumba na Shekarar 2021, zata fara bada rigakafin cutar na Moderna ga wadanda basu karbi rigakafin, inda ya bukaci Yan Jahar da suyi amfani da damar wajen karbar rigakafin cutar.
Yace “Jahar Edo, a cikin awanni 72, ta samu mutane 5 da suka mutu daga cutar Covid-19, dukkanin su ba’a yi masu rigakafi ba, inda ya jaddada bukatar kowa da yaje ayi mashi rigakafin, domin ya zamanto cikin koshin lafiya da cigaba da rayuwa.
“Mun kuma tabbatar da sabbin mutane 58 wadanda suka kamu da cutar, tare da mutane 52 da suka warke, gami da mutane 616 wadanda suke fama da cutar da ake yiwa magani a cibiyoyin kula da masu cutar a cikin Jahar.
Ya ce Jahar a cikin kashi na uku na cutar, ta yiwa mutane dubu 14,898, tare da samun mutane 1,270 masu fama da cutar, a yayinda da mutane 590 suka warke.
Comments 1