Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC sun kama wasu mutane 18 da ake zargi da damfarar yanar gizo a Abuja.
Wadanda ake zargin sun hada da Innocent Samson, Obiora Eze, Ifeanyi Joseph, Isidore Chinedu, Badaki Linus, Ameh Nick, Kelvin Chima, Akwa Iwu Promise Ifeanyi, Adekunle Samuel.
Sauran sun hada da Abutu John, Testimony Mathiew, Omale Mary Ochanya (mace), Afam Darlington Edwin, Henry John, Urochukwu Abel, Ogieto Gift, Innocent Gideon, Ojimini Maduemyi Raymond, Mathiew Timothy, da Kingsley Chukwuemeka.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na Twitter ta ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar 19 ga Yuli, 2022, a rukunin runduna ta biyar dake, Kurudu a babban birnin Tarayya Abuja, biyo bayan rahotannin sirri da hukumar ta samu kan zarginsu da hannu a zamba ta yanar gizo.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da motoci uku kirar: Lexus RX 350, Lexus ES 350, da Peugeot 306, babur, kwamfutoci guda shida, da wayoyin hannu.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawan ta kara da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya bayan an kammala bincike.
A wani labarin kuna na daban.
Alkalin Alkalan Jihar Ekiti Ya Yi Wa Fursunoni 34 Afuwa
A ranar Alhamis ne babban alkalin jihar Ekiti, Justice Adeyeye Oyewole, ya saki fursunoni 34 a gidan yari na Ado Ekiti.
Babban Alkalin da ya isa cibiyar gyaran hali ya leka wurin tare da yaba wa jami’an gidan gyaran halin na Ekiti bisa yadda suke kuka tsaftar muhalli.
Mai shari’a Adeyeye ya yi nazari sosai kan shari’o’in fursunoni 508 da ke zaman jiran shari’a a gidan yari tare da sakin 34 daga cikinsu.
Kwanturolan hukumar gyaran hali na kasa da ya samu wakilcin mataimakiyar kwanturola Atinaro Titus, ya yabawa babban alkalin jihar ta Ekiti bisa wannan karimcin da ya nuna, wanda yace zai taimaka matuka wajen kwantar da hankulan fursunonin da har yanzu basu samu ‘yancinsu ba. da kuma sake farfado da fatan su na alheri a nan gaba.
Ya kuma yi kira ga alkalan kotun da su yi amfani da hukuncin domin rage cunkoso a wurin.
Atinaro ya shawarci fursunonin da suka sami ‘yancinsu da su kasance masu bin doka da oda.
Wadanda suka halarta a wajen taron sun hada da alkalan babbar kotun jihar, alkalai, jami’in ACC Alagbe O.T da ke kula da gidan yarin Ado Ekiti.