Daga: Abbas Yaura
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta kama wasu mutane 45 da ake zargi da damfarar yanar gizo daga yankin Trans Ekulu a jihar Enugu.
Kakakin Wilson Uwujaren ya bayyana sunayensu a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Wadanda ake zargin su ne Paschal Tochukwu, Eze ifeanyi, Raphael Chukwuemeka, Kenneth Akwozo, Obodoeze Samson, Michael Chidiebere, Ogbu Chekwube, Edeh Peter, Nweze Ifeanyi, Emeka Nwankwo, John Chibuike.
Sauran sun hada da: Onyedikachi Samuel, Ikenna Chijioke, James Tochukwu, Uche Obieze, Ekwunife Chinonso, Chukwuebuka Ogbonna, Chinedu Ephraim, Emmanuel Nnaji, Ychenna Nweke, Orji Chisom, Eze Emmanuel, Michael Chidere.
Rashin Tsaro Babbar Barazana Ce Ga Zaben 2023 – Tsohon Hafsan Soji
Emmanuel Chidere, Chijioke Ugwu, Ugwuoko Obinna, Emeka Obilo, Mbah Ebube, Onah Kasie, Ikechukwu Michael, Oferka Frank, Onyia Joseph, Amagba Tochukwu, Ogbuabor Emmanuel, Michael Obi.
Kana Sauran sun hada da Nwokeji Joshua Chetachukwu, Nzube Daniel. Stephen Ogbuabor, Sunday Dimeze Chidi, Ebuka Ilouno, Adimoranma Christian, Godwin Chukwuemeka, Nnamezie Chidi, Bright Chineme, Vitus Makwe.
An gano motocin alfarma guda biyar, wayoyin hannu da dama, kwamfutocin tafi da gidanka, da dai sauran kayayyaki da ban daban.
Kazalika Hukumar ta kuma bayyana cewa, Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
A wani labari kuma na daban.
Ku Yi Watsi Da Masu Wa’azin Da Ka Iya Tarwatsa Najeriya— IBB
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bukaci kafafen yada labarai da su yi watsi da masu wa’azin rashin hadin kai, su kuma baiwa masu kokarin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai muhimmanci.
IBB ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya a wani katafaren gidansa da ke Minna.
Ya ce dole ne ‘yan Najeriya su dage wajen yin imani da hadin kan Najeriya tare da rokon su da su yi hakuri da kuma yi wa kasa addu’a domin ya shawo kan kalubalen da ke addabar kasar nan
Yayin da yake nuna jin dadinsa kan rawar da kafafen yada labaran Najeriya ke takawa, ya yi kira da a sauya fasalin yada wasu labaran domin samun ingantacciyar Najeriya ta hanyar yin abin da ya dace.
Dattijon ya kuma yabawa masu aikin yada labarai a kasar nan kan yadda suke gudanar da ayyukansu na ban mamaki a cikin rahotonsu, nazarin batutuwa da goyon bayan dimokuradiyya mai dorewa wanda dole ne a inganta ta hanyar tafiyar da al’umma.
Tsohon shugaban na mulkin sojan ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu so, jajircewa, rikon amana da addu’a domin kawo karshen kalubalen rashin tsaro da al’ummar kasar ke fuskanta a halin yanzu, inda ya kara da cewa wadanda ke bayan wadannan matsaloli za su gane illar dake tattare da tasirin ayyukansu.