Hukumar EFCC ta ce ta kwato karin kudi har Naira miliyan 900 na shirin inshorar lafiya ta kasa.
Kakakin hukumar Mista Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar.
KU KARANTA: Dattawan Arewa Sun Musanta Zaɓar Atiku A Matsayin Ɗan Takarar Su
Ya yi zargin cewa kudaden wani bangare ne na kudaden da wasu bankunan suka suka yi wata sabatta juyatta da su, bayan da suka rike kudin tun a shekarar 2015 kuma suka ki tura su cikin asusun bai daya na NHIS.
A cewar sa, kudaden da aka kwato an mika su ga NHIS a ranar 8 ga watan Fabrairu.
Ya kara da cewa, a ranar 10 ga Fabrairu, 2022, hukumar ta saki naira biliyan 1.5 da ta kwato daga bankuna ga shirin inshorar lafiya ta kasa.
Haka kuma a ranar 5 ga watan Agustan 2022 hukumar ta saki Naira biliyan 1.4 ga shirin.
A ranar 29 ga watan Yuli, 2021, babban sakataren hukumar ta NHIS, Farfesa Muhammad Sambo, ya yabawa hukumar EFCC bisa taimakon hukumar ta NHIS wajen kwato kudaden da suka makale a bankunan kasuwanci.
A wani labarin kuma: 2023: Atiku Ya Samu Kakkyawar Tarbar Jama’a Ya Yin Yakin Neman Zabe a Adamawa
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya yi kira da a kada kuri’a ga daukacin ‘yan takarar jam’iyyar a babban zabe mai zuwa.
Abubakar ya yi wannan kiran ne a babban taron yakin neman zaben sa na shugaban kasa da aka gudanar a Yola, mahaifar kakansa, ranar Asabar.