Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta musanta kai simame gidan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu.
Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya ce ikirarin kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Legas da hukumar ta yi ba gaskiya ba ne.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Shugaban APC Na Kasa Ya Shiga Ganawa Da Gwamnoni 10
“An jawo hankalin hukumar EFCC kan wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani, cewa jami’an hukumar sun kai samame gidan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa mai zuwa, inda suka kwato makudan kudade har Naira biliyan N400bn.
“Hukumar tana so ta bayyana cewa babu wani aiki irin wannan da EFCC ta yi.
“An umarci jama’a da su yi watsi da rahoton a matsayin labaran karya,” in ji shi.NAN
A wani labarin kuma, Duk Satar Da Ku Ka Yi Yanzu Ba Ta Da Amfani — Kwankwaso Ya Caccaki Gwamnonin Da Ke Sukar Buhari
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP), ya caccaki gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari kan batun sake fasalin kudin Naira.
Babban Bankin Najeriya (CBN) wanda ya gabatar da manufar a bara ya sanya ranar 31 ga watan Janairu a matsayin wa’adin kashe tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1000 a bainar jama’a.