Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta saki kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo bayan shafe sa’o’i 48 a hannun ta.
Oluomo dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Ifo ta 1 a majalisar dokokin jihar Ogun ya koma gidansa dake Ifo a safiyar ranar Asabar din nan.
Daruruwan magoya bayansa ne suka tarbe shi wadanda suka hada da shugabannin kungiyar kiristoci ta Nijar a Ifo.
KARANTA ANAN: Ban Taba Cewa Wike Ba Uban ‘ya’yansa Bane – Shugaban PDP Ayu
Wani mai taimakawa shugaban majalisar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce kakakin da jami’an hukumar EFCC suka dauke shi a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas a ranar Alhamis ya dawo gida da safiyar Asabar.
Ya ce, Ogansa ya dawo Yanzu haka yana gidansa dake Ifo. An mayar da gidansa wani filin dandano sakamakon yadda ake tururwar zuwa don tarbarsa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa An kama Oluomo ne bisa zargin sama da fadi da dukiyar al’ummar dake yake wakilta.
A wani labarin kuma: Najeriya Mabudi Ce: Kamala Harris Ta Karin Bakuncin Osinbajo A Fadar White House.
Mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris ta karbi bakuncin takwaranta na Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo a fadar White House dake birnin Washington DC.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Kasashen biyu sun gana ne domin tattauna alakar Najeriya da Amurka da kuma shirin mika wutar lantarki a Najeriya, a cewar sanarwar daga sassan biyu.