Jami’an Hukumar Yaki cin hanci da rashawa da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa EFCC a yau Litinin sun kai farmaki a hedikwatar Hukumar Raya Biranen Jihar Kaduna wato KASUPDA inda suka yi awon gaba da Babban Daraktan Hukumar, Malam Ismail Umaru Dikko.
Hukumar KASUPDA tayi kaurin suna a jihar Kaduna, saboda rushe kadarori da ta ke yi a fadin jihar.
Shugaban Hukumar Dikko, mataimaki ne na musamman ga gwamna Nasir El-Rufai, kafin a daga matsayinsa zuwa shugaban hukumar KASUPDA a shekarar 2019.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Baban Daraktan na cikin ganawa da ma’aikatan sa lokacin da jami’an EFCC suka karbe ikon da harabar ofishin mintuna kadan bayan karfe 10 na safen yau litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya za ta Gina Cibiyoyin Nakasassu a Jami’o’i 4 dake Nigeria
Shaidun gani da ido sun ce an samu tashin hankali kafin DG ya shiga wata bakar mota kirar Toyota mallakin Hukumar ta EFCC.
Majiyoyi da dama sun ce, jami’an EFCC guda biyu cikin shigar Girma, tare da jami’an ‘yan sanda biyu dauke da bindigogi sun tasa keyar shugaban KASUPDA zuwa cikin motar su.
Majiyar ta ce tun da farko ma’aikatan KASUPDA sun yi kokarin hana EFCC fita da Shugaban na KASUPDa, kuma jami’in tsaro a kofar Ma’aikatar ya hana motar fita.
Sai dai daga bisani Isma’il Dikko ya umarci jami’in tsaron dake kula da kofar ma’aikatar da ya buɗe ƙofar.