EFCC tace Kotu ta yanke wa Dubban Masu Laifi data gabatar a cikin watanni masu yawa
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, a ranar Laraba, ta bayyana cewa ta sanya an zartar wa jimillar mutane 2,210 hukunci da ake zargi da aikata laifukan tattalin arziki da hada-hadar kudi tsakanin 1 ga Janairu, 2022, zuwa 5 ga Agusta, 2022.
Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka, a yayin wani taron karawa juna sani da ‘yan jarida mai taken, “tabbatar da kawo sahihan rahotanni na masu yaƙi da masu yiwa ƙasa ta’annati” wanda aka gudanar a hedikwatar EFCC, da ke Abuja..
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Ceto Mutane 6 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
Wannan ya zo ne kimanin watanni takwas bayan da hukumar EFCC ta sanar da cewa ta samu nasarar ganin an zartar wa masu laifuka 2,220 hukunci akan Laifuka daban-daban a shekarar 2021.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta PUNCH ta ruwaito cewa, wannan hukunce-hukunce da aka yanke shine wanda Hukumar ta tabbatar anyi mafi girma tun lokacin da aka kafa ta, an samu karin kashi 127.5 cikin 100 daga laifuka 1,280 da hukumar ta samu a shekarar 2019.
Da yake jawabi a taron bitar, Bawa ya ce, “Wasu daga cikinku za su tuna cewa a karshen shekarar 2021, hukumar ta bayyana cewa ta samu jimillar masu laifuka 2220. Ina mai farin cikin sanar da ku cewa, a shirye muke mu inganta wannan adadi kamar yadda rahoton yanke hukunci ya zuwa ranar 5 ga Agusta, 2022, ya kasance 2210.
“Duk da haka, wata nasara da yawancin ku ba za ku iya gane ta cikin sauƙi ba ita ce tasirin sa hannun EFCC a kasuwar Forex ya ɗaga darajar Naira.
“Ina kuma kira gare ku da ku ƙara inganci a bincikenku a wannan fanni domin yana da amfani ga hadin kanmu mu samu kudin kasa wanda kimarsa ba ta bin son zuciya na karkatattun masu hasashe.