Shahararren matashin ɗan wasannan na gaba wanda yake fafata wasansa a gasar Bundes Liga ta ƙasar Jamus kuma wanda yake murza leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Brussia Dortmund wato Eirlin Braut Haaland ya fara kafa tarihi a ƙasarsa ta haihuwa wato Norway.
Haaland ya fara kafa tarihinne bayan da ya samu naaarar jefa ƙwallaye guda 3 a raga a daren ranar Lahadi kuma wannan shine karon farko da ɗan wasan ya samu nasarar jefa ƙwallaye guda uku rigis wa ƙasar tasa ta haihuwa tun bayan da ya fara fafatamata wasa a matsayinsa na babban ɗan wasa.
A wasan da Norway ta fafata a daren na jiya ta ragargaza Romania daci 4 da nema inda daga cikin ƙwallaye guda 4 da aka jefa a faga Eirlin Braut Haalan ne ya samu nasarar jefa guda 3 rigis a raga. ƙasashen na nahiyar turai dai suna fafata wasannin gasar neman cancantar buga gasar cin kofin nahiyar turai ne.
Jaridar www.dimokuradiyya.com.ng ta gudanar da wani bincike akan Haaland inda ta gano cewar kusan kowanne wasa sai ya jefa ƙwallo kama daga ƙungiyar ƙwallon ƙafan da yake fafata wasansa da kuma yadda yake wakiltar ƙasarsa ta haihuwa wato Norway. Shidai a halin yanzu idan aka magutse da wasannin da ya bugawa ƙasar tasa da kuma wasannin da ya bugawa ƙungiyoyinsa za a iya cewa.
Haaland ya buga wasanni guda 48 inda ya sami nasarar jefa ƙwallaye guda 51 a raga inda ya jefa wasu da ka sannan ya jefa wasu da ƙafarsa ta hagu haka zalika ya sami nasarar jefa wasu ƙwallayen da ƙafarsa ta dama, sai dai za a iya cewa ƙwallayen da ya jefa da ƙafar dama sunfi yawa daga cikin ƙwallaye 51 daya jefa.
Haaland dai matashin ɗan wasa ne mai ƙwazo sosai wanda baya wasa idan ya sami damar jefa ƙwallo. Sai dai har yanzu duk da bai daɗe da komawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Dortmund ba manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a nahiyar turai sunaci gaba na nuna sha’awarsu ta sayensa ciki harda ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid.