Matasan Jam’iyyar PDP na Jahar Ekiti sun yi kira ga shugabanni da masu ruwa da tsaki dasu zama masu samar da zaman lafiya, domin samun nasara zaɓen fidda gwani, wanda zai sanya a zaɓi ɗan takara da zai iya cinye zaɓen Gwamna a ranar 18 ga watan Yuni.
Matasan ƙarƙashin ƙungiyar neman samun nasarar zaɓe ta Najeriya, wanda suka ce aiki a tare zai sanya a samu nasarar zaɓe, sun bayyana cewa haɗin kai a tsakanin mambobin jami’iyyar dole ne, idan har dagaske Jam’iyyar naso ta samu nasara akan Jam’iyya mai mulki a Jahar Ekiti.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Dage Sauraren Karar Wanda Ya Kashe Hanifa, Yayin Da Kotu Ta Iza Keyarsu Gidan Yari
Shugaban Ƙungiyar Seyi Ajibola wanda yayi jawabi a Ado Ekiti a lokacin wani taro na zaman lafiya da ƙungiyar ta shirya, domin bada shawara ga Jam’iyyar akan hanya mai ɗorewa, ta buƙaci ƴan takarar da sauran masu ruwa da tsaki dasu ajiye makaman su, su rungumi zaman lafiya.
Yace ” muna da ayyuka sosai a PDP ta Ekiti, domin idan ba’ayi kyakkyawar kula ba, baza’a samu nasara ba duk wani ɗan takara da aka sanya a gaba. Dole mu ajiye faɗan cikin gida da ra’ayoyin mu.
Ajibola wanda yace bazasu sanya kansu akan dukkanin Shuwagabannin Jam’iyyar, yace “abunda muke so shine su ajiye bambance-bambance domin cigaban Jam’iyyar.