By Abbas Yakubu Yaura
Wata babbar kotun jihar Ekiti da ke yankin Ado Ekiti ta yanke wa wani Yarima mai jiran gado, Ademola Omoniyi mai shekaru 42 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe basaraken al’ummarsa.
An gurfanar da Omoniyi ne a kan tuhumar kisan kai da ya saba wa sashe na 316 da kuma hukunta shi a karkashin sashe na 319 na kundin laifuffuka, C16, na Dokokin Jihar Ekiti ta Najeriya shekarar 2012.
Sauya Sheka: Kotun Ta Haramtawa INEC Gudanar Da Zabe A Mazabar Michikan Jihar Adamawa
Laifin ya kara da cewa, “Ademola Stephen Omoniyi a ranar 20 ga watan Agustan shekarar 2018, a Odo Oro Ekiti a sashin shari’a na Ikole Ekiti, ya kashe mai martaba, Oba Gbadebo Ibitoye Olowoselu ll, Onise na Odo Oro Ekiti a karamar hukumar Ikole ta Ekiti.”
Wani basarake wanda ya bada shaida a gaban kotun ya ce, “Mun kasance a fadar ne a ranar domin taron zartarwana Onise-in-Council da misalin karfe 7 na safe. Kafin a fara taron, Ademola Omoniyi ya shiga fadar, ya zauna a kan kujerar kabiyesi, amma sarakunan sun fusata da matakin da ya dauka suka kore shi.
“Bayan ganawar, marigayi Onise, tare da ma’aikacin sa, suna tattaki zuwa babban fada, sai Ademola ya fito daga maboyarsa, ya kai wa kabiyesi hari da wuka a kan hanya, ya kuma kashe shi. Kafin wannan rana, ya kasance yana nuna kansa a matsayin sarkin garin.”
Domin tabbatar da karar sa, Lauyan jihar, Adegboyega Morakinyo, ya kira shaidu biyar, ya kuma gabatar da rahoton lafiyarsa, da bayanan wanda aka yankewa laifin, wuka da igiya, da dai sauransu, kamar yadda aka nuna, yayin da mai laifin ya yi magana ta bakin lauyansa, Tope Salami, da kuma kiran bada shaida.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Olukayode Ogundana ya yi watsi da ikirarin cewa wanda ake tuhumar mahaukaci ne.
“Saboda haka, wanda ake kara, Omoniyi Ademola Stephen, an yanke masa hukuncin kisa kuma za a rataye shi har sai ya huce.” Alkalin ya kara da cewa.
Comments 1