Ɗan Takarar Gwamnan Kaduna Kuma Sanatan Tsakiya, Sanata Uba Sani ya bayyana rashin jindaɗin sa na yadda ake yawaitar samun Kashe-kashe a duk rana a Najeriya, sakamakon harin ta’addanci, yana mai cewa Gwamnati bazata zauna a haka ba, dole ta kawo ƙarshen shi.
Sanatan yace Gwamnan Jahar Nasir El-Rufa’i na bakin ƙoƙarin sa wajen ganin ya samar da tsaro a Jahar, inda yace zasu yi bakin ƙoƙarin su na ganin sun mara masa baya domin samun zaman lafiya a Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane Bakwai Sun Mutu Sakamakon Ta Tashin Gobara A Wani Gidan Mai A Jihar Jigawa
Ɗan takarar Gwamnan jihar kaduna Kuma Sanatan Tsakiya Sanata Uba sani Ya bayyana wannan cikin wata sanarwa a lokacin da yake godiya ga tsohon Gwamnan jihar Lagos Asiwaju Bola Tinubu Bisa ziyarar daya Kai Jahar Kaduna domin jajantawa kan harin ta’addanci da Ƴan bindiga suka aiwatar kan matafiyan cikin jirgin Ƙasa na Abuja zuwa kaduna.
Sanarwa tace “A safiyar yau ne na bi sahun Gwamna Nasir El-Rufa’i wajen tarbar jagoran jam’iyyarmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ziyarar da ya kawo Kaduna domin jajanta wa Gwamnan mu da ilaharin al’ummar Jihar Kaduna, bisa harin jirgin ƙasa akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
A cewar Uba Sani “Tun da farko Asiwaju Bola Tinubu ya nuna tausayawa da kuma nuna kishin Ƙasa, ta hanyar soke taron sa na murnar ranar haihuwarsa na shekara-shekara da ya Saba gabatar wa,
“Wannan soke taro dai ya faru ne domin karrama waɗanda harin jirgin ƙasa ya rutsa da su, lamarin da ba kasafai ake samunsa ba wanda kuma ya kasance mai girman gaske”.
Sanatan ya ƙara dacewa “Hare-haren Kaduna sun dame mu baki daya. Gwamna ya kasance a sahun gaba wajen samar da mafita masu amfani wadanda ake aiwatarwa sannan kuma na yi ta bayar da shawarwari tare da tura ƙudiri a Majalisar Dattawa da nufin magance wannan matsalar.
“Ina son yin amfani da wannan damar domin in jinjinawa Asiwaju Bola Tinubu bisa yadda ya dauki lokaci ya ziyarci Jihar Kaduna da kuma tausaya wa al’ummar jihar” Cewar Sanata Uba Sani