Gwamnan Jahar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya bayyana dalilan da suka sanya aka cire Shugaban Ma’aikata Muhammed Sani Abdullahi, da kuma mai dashi Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren a matsayin Kwamishina.
Gwamnan yace tun bayan Sani ya bar ma’aikatar shekaru biyu da suka gabata, Gwamnati ke fama da matsalar haɗa kasafin kuɗi.
Yana jawabi ne a lokacin tattaunawa da kafafen yaɗa labaru a Jahar da kuma saƙon murya da Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta samu, inda yace cire Shugaban Ma’aikata baya da nasaba ko kaɗan da kiran Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, a matsayin tsohon Sarki a wani taro da aka shirya a Jahar.

KARANTA WANNAN LABARIN: Mambobin Majalissa 6 Ba Zasu Iya Tsige Shugaban Majalissa Ba– Dan Majalisar Wakilai Na Jihar Filato
El-Rufa’i ya bayyana abinda ya faru tsakanin tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi da Abdullahi, a matsayin wasan da aka daɗe ana yi, tsakanin mutanen Zariya da Kano, a yayinda ƴan Zaria ke kallon Kanawa a matsayin bayin su.
Ya bayyana waɗanda suke alaƙanta canje-canje na Gwamnatin sa da wasan da ya faru, a matsayin sun kasa fahimtar gwamnati.
Yace canje-canjen anyi shine domin inganta ƙarfin gwamnatin sa, na kai mutane inda zasu fi bada gudummawar da zai taimakawa gwamnati tayi aiki yanda ya kamata.
Gwamnan ya ƙara dacewa, dangantakar shi tsakanin shi da Sanusi a Matsayin bada shawara, bawai ya koya masa yanda zai gudanar da gwamnatin sa ba.
“Shine Shugaban Jami’ar Jahar, sabudda yana ƙwarewa akan haka. Kuma shine Mataimakin Hukumar Saka hannun jari ta Jahar wato-KADIPA, kuma waɗannan ne wurare guda biyu daya ke taimakawa da shawara, kowa yasan Sanusi a Matsayin ƙwararren masanin tattalin arziki.
Comments 1