Wata sanarwa da ta fito daga mai taimaka wa Gwamna Nasiru El-Rufai a kan al’amurran yada labarai, Muyiwa Adekeye ya nuna cewa wasu Karin mata 2 sun samu sabbin mukamai a gwamnatin. Matan suna daga cikin mutane 17 din a ka nada a ranar tarlatan da ta gabata.
A cewar sakon Stella Amako it ace yanzu SA Community Relations sai kuma Hajiya Zainab Shehu, SA Social Development.
Takardar ta nuna da cewa 5 daga cikin mutanen da gwamnan ya nada mata ne, inda wasu zasu yi aiki a matsayin manyan mataimaka na musamman da kuma mataimaka na musamman ga gwamnan.
Sauran su ne Aliyu Haruna, a harkokin matasa; Ibrahim Ismail, mu’amala da mutanen kauyuka; Hafsat Ashiru, tsare-tsare, and Nazir Sanusi, fasahar zamani.
Sannan akwai Mohammed Shuaibu, Yakubu Yatai, Ibraheem S Musa, Ashiru Zuntu, da Rabi Manchi.
Daga bisani kuma akwai Mahmud Aminu, Aminu Lawal Na-Anty, Sonia Bature, Kamal Aliagan, da Sakinat Bello.
Dukkansu za su rika aiki ne akan abi da ya shafi hulda da jama’a, muhalli da kuma bada shawara akan shari’a.