El-Rufa’i ya shimfiɗa ayyukan cigaba a Kaduna, nima zan ɗora daga haka — Cewar Sanata Uba Sani
Sanata Mai Wakiltar Kaduna ta Tsakiya Sanata Uba Sani ya bayyana cewar, Gwamna El-Rufa’i ya shimfiɗa ɗumbin ayyukan cigaba a Jahar, kuma a shirye yake ya ɗora mulkin sa ta hanyar kawo cigaba masu tarin yawa.
Sanatan ya bayyana haka ne a jiya lahadi a lokacin da yake yawon rangadin tuntubar masu ruwa da tsaki na jihar Kaduna, a ƙoƙarin sa na tsaya wa takarar Gwamnan jihar Kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: IPOB Ta Musanta Zargin Kona Gidan Shugaban Ohaneze
Sanatan yace “A yanzu haka ina kan tuntuɓar masu ruwa da tsaki a faɗin jihar Kaduna, wanda a halin yanzu muka taru a yau”.
Uba Sani yace ya samu gagarumar nasara a ziyarar daya kai a ƙananan hukumomin Ikara, da Kubau, da Lere da kuma Soba, Wanda acewar sa hakan wata manuniya ce dake cewa al’umma nason ya zama Magajin Gwamna Nasir El-Rufa’i.
” Zan cigaba da gina gadon mulkin Gwamna El-Rufai na cigaban ababen more rayuwa da ya faro, magance manyan kalubale, da kuma kasancewa mai gaskiya, rikon amana da jajircewa wajen gudanar da mulki”, Inji shi.
Sanata Uba Sani ya Ƙara dacewa zai kasance mai ƙirƙire-ƙirƙire da kuma shimfiɗa mulki mai ɗauke da kishin jama’a da haɗin kai.
Shuwagabannin kananan hukumomi da masu unguwanni, manyan jiga-jigan jam’iyyar da magoya bayana masu kishin sun kasance a wajen domin tarbarta da sauraren sakon ci gaban da nazo dashi.
Uba Sani ya yabawa Al’umma akan ƙoƙarin su na cigaba da yaɗa manufar shi yana mai cewa Shuwagabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi sun kai ziyarar gani da ido domin ganin jam’iyyar APC ta bashi tikiti a zaɓen Gwamnan jihar Kaduna a shekarar 2023.
“Godiya ta ga shugabannin ƙananan hukumomi hudu da na ziyarta a yau da kuma manyan shugabannin jam’iyyar mu da suka yi min rakiya” Cewar Sanata Uba
Waɗanda suka yi mashi rakiya Sun haɗa da Hon. Salihu Sadiq Ibrahim (Ikara LG), da Hon. Bashir Suleiman Zuntu (Kubau LG), Hon. Abubakar Buba Lere (Lere LG), Hon. Abubakar Mamadi, tsohon dan majalisar tarayya, Hon Bashir Zubairu, tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna.
Akwai kuma Hon. Aminu Shagali (Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Hon. Ahmed Chokali, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Hon. Yakubu Soja, Tsohon Dan Majalisar Kaduna, Honarabul Hayatu Usman, Tsohon Dan Majalisar Jihar Kaduna. Majalisar, Hon Kabiru Jarami, Shugaban Majalisar Kaduna ta Kudu L/G, Hon Muktar Baloni, Shugaban Kansila na Kaduna ta Arewa L/G.
Sai Hon Jaja, Shugaban Majalisar Kudan L/G, Hon Abubakar Shehu, Shugaban Majalisar Giwa. L/G, Hon Abubakar Master, tsohon shugaban Sabon Gari L/G, Hon Nasiru, mataimakin shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa L/G.
Sanata Uba sani dai na daya daga cikin manyan Yan majalisar Dattijan Nageriyasu karfin Iko da fada aji musamman yadda ya kasance mutun Mai Taimakon Al’ummar sa.