Sojoji sun kashe wani fitaccen kwamandan ‘yan ta’adda, Dogo Maikasuwa, a wani dajin da ke yankin Gengere-Kaso, daura da kan iyakar Chikun da Kajuru a jihar Kaduna. Kamar yadda Punch ta ruwaito
Dogo Maikasuwa, an ruwaito shi ne, ya jagoranci wasu munanan hare-hare a kananan hukumomin Chikun da Kajuru na jihar, wadanda ayyukan ta’addanci suka fi shafa a tsawon shekaru.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Ten Hag Ya Yanke Shawarar Saida Maguire
Kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a, ya ce fitaccen kwamandan ‘yan ta’addan tare da Dakarun sa sun yi musayar wuta da sojojin kwanton bauna inda ya gamu da ajalinsa.
A cewar kwamishinan, Mambobin Yan ta’addada da dama da ‘Dogo Maikasuwa’ ke jagoranta ne suka tsere zuwa cikin dajin da raunukan harbin bindiga.
“Sauran ‘yan fashin sun tsere da raunukan bindiga. An kuma labarato cewa daya daga cikinsu ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a wannan kazamin fadar,” inji shi.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun ‘yan ta’addan a cewar kwamishinan sun hada da bindiga kirar AK-47 guda daya, kunshin Alburusai guda daya, babura biyu da kuma rigar soja guda daya.
Wannan ci gaban, in ji kwamishinan, ya faranta wa gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa’i rai, inda ya yaba da kwazon sojojin.
A WANI LABARIN KUMA: Mane ya shiga tawagar ƙasar Senegal don zuwa Qatar 2022
Ɗan wasan tsakiyar tawagar kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta ƙasar Jamus, wato Sadio Mane ya shiga cikin tawagar yan ƙasar a gasar kofin Duniya na shekarar 2022 a ƙasar Qatar.
Mane, Mai shekaru 30 a baya an yi fargabar ba zai halarci gasar ba sakamakon raunin da ya samu a wasan da ƙungiyar sa ta Bayern da ta fafata a gasar Bundesliga na karshen mako