Gwamnan Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna a yau Litinin ya yi Allah Wadai da harin da aka kai a garin Madamai dake Karamar hukumar Kaura na jihar, Wanda ya yi sanadiyar mutuwar akalla Mutum 34.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran yau da kullun Mr Samuel Aruwan ya fitar a jihar, Gwamnan ya yi alkawarin cewa, Gwamnatin jihar ka iya daukar dauyin kula da lafiyar wadanda suka sami raunika sanadiyar harin.
El’Rufa’i ya Kuma umarci Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, da ta ziyarci inda lamarin ya faru, domin tallafawa iyalan wadanda lamarin ya shafa.
Kazalika ya kuma jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, inda Kuma yayi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka Mutum.
KARANTA WANNAN LABARIN: NDLEA ta gurfanar da Mai shekara 28 a gaban Kotu, bisa safafar Tabar Wiwi
A karshe ya kuma bukaci al’umar yankin da su kwantar da hankulansu, ya kuma hori jami’an tsaro da su yi duk Mai yuwa, wajan bankado wadanda ke da hannu a cikin harin.
A wani cigaban Kuma
Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta ta ce ta cafke wasu mutane takwas da ake zargi yan fashi da makami ne da ke addabar mazauna karamar hukumar Keffi ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda a jihar, ASP Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan, a wata hira ta musamman da manema labarai sukayi da shi garin Lafia, babban birnin jihar, a jiya Lahadi.
Ya ce ankama wadanda ake zargin ne tare da jagoran su Mai suna Shamsu Usman, wanda shine ake zargin ya jagoranci farmakan wani gida a unguwar Angwan Jarmi na karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa.
Kazalika ya ce, jami’an rundunar yan sandan sun kuma cafke wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, wadanda ake zargin sun sace matar wani Mai suna Alhaji Ibrahim Sarkinnana a kauyen Ayongo da ke karamar hukumar Awe ta jihar.
Comments 1