By Ishaq Dabai
Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya jajantawa Cocin Evangelical Winning All ECWA yayin da ‘yan bindiga a safiyar ranar Lahadi suka farmaki masu ibada a cocin, inda suka kashe mutum guda tare da jikkata wasu.
Lamarin ya faru ne a Cocin ECWA, Gabaciwa dake karamar hukumar Kachia.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kwamishinan Tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, yace El-Rufai yayi Allah wadai da harin cikin kakkausan harshe, inda ya bayyana shi a matsayin manufar raba kawunan masu aikata miyagun laifuka dake amfani da addini.
A cewarsa,”Jami’an tsaro sun kai rahoto ga Gwamnati cewa harin ya faru ne a Cocin ECWA, Gabaciwa a karamar hukumar Kachia. A cewar rahoton, an rasa rai daya kuma wasu masu ibada sun samu munanan raunuka, wadanda aka garzaya da su asibiti.“Hukumomin tsaro suna samun karin bayanai, wanda gwamnati za ta sabunta wa jama’a a kan kari.
“Gwamnan, wanda ya nuna bacin ransa a kan lamarin, ya bayyana shi a matsayin mummunan aiki da aka kai wa ‘yan kasa marasa laifi da ke amfani da hakkokinsu na kundin tsarin mulki na duniya na ‘yancin addini.
“Gwamnan wanda dake jiran ƙarin rahotanni kan lamarin ya umarci Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Kaduna data tantance yankin tare da bada taimako ga waɗanda abin ya shafa da ke samun kulawar likitoci yanzu haka.
“kazalika, Gwamnan ya yi ta’aziyyar ga iyalan wani mai suna Nasiru Abdullahi na Gobirawan Kamacha a yankin Bina na karamar hukumar Igabi wanda ‘yan bindiga suka kashe.gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan sa.