Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-rufa’i ya ce gwamnatin jihar yanzu haka na duba yiwuwar tashin wasu garuruwa guda biyu dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
El-rufa’i ya ce zasu tashi mutanan yankunan ne saboda yadda ake ci gaba da samun masu bayar da bayanai ga yan bindiga, wadanda suke ci gaba da cin kare su babu babbaka akan hanyar.
Garuruwan da ake duba yiwuwar tashin su sune kamar haka: Rijana, Kateri, Akilibu, wadanda baki dayan su suna kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ne.
Gwamna Nasir ya kara da cewa mafi yawan garkuwa da mutanen da bata garin ke yi yana faruwa ne a wadannan tsuki, a dan haka dole ne a san abunyi akan ƙauyukan.
A cewar sa, sun samu rahotannin sirri daga jami’an tsaro, wadanda suke cewa akwai wasu daga cikin mutanen garin, dake aiki tare da yan bindiga.
Wannan jawabi na Gwamnan Kaduna na zuwa ne a yayin taron kwamitin tsaro na jihar, na watanni gudun farkon shekarar 2022, wanda ya samu halartar Kwamishinan harkokin tsaro na jihar Samuel Aruwan.