Elon Musk a ranar Litinin 6 ga watan Fabrairun 2023, ya samu $3.9bn (N1.81trn) wanda hakan ya sanya samu N4.45trn ($9.8 billion) a mako guda.
Kuɗin da Elon Musk ya samu a ranar Litinin sun fi gabaɗaya kasafin kuɗin N1.76trn na shekarar 2023 na jihar Legas. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Tirƙashi: Bidiyon wata budurwa mai aski da falleliyar wuƙa ya ɗauki hankula
Shugaban kamfanin na Tesla yanzu dukiyar sa ta kai $188.1bn saɓanin $178.3bn da take a watan Janairun 2023, a cewar Forbes.
Wannan farfaɗowa da Musk yayi na nufin yanzu saura $29.1bn ya kamo Bernhard Arnault, attajirin da yafi kowa kuɗi yanzu a duniya.
Ya zuwa ranar Litinin 6 ga watan Fabrairu, dukiyar Bernhard Arnault ta kai $217.2bn.
Elon Musk ya fara watan Fabrairu da ƙafar dama, idan akayi duba da yadda ya fara watan Janairun 2023.
Ya zuwa ranar 1 ga watan Janairu, 2023, jerin Forbes na attajiran duniya ya bayyana cewa Musk yana da dukiyar da ta kai $136.9bn. A ɓangare ɗaya kuma Arnault yana da dukiyar da ta kai $183.0bn. Tazarar dake tsakanin su ta kai ta $46.1bn.
Wannan farfaɗowa da Musk yayi na nufin cewa nan da wasu ƴan makonni masu zuwa, Elon zai koma matsayin sa na attajirin da yafi kowa kuɗi a duniya.
Jerin attajiran da suka fi kowa kuɗi a watan Fabrairu a duniya
- Bernard Arnault da iyalansa- $217.2bn
- Elon Musk- $188.1bn
- Jeff Bezos- $125.2bn
- Larry Ellison- $113.7bn
- Warren Buffett- $107.0bn
- Bill Gates- $105.2bn
- Carlos Slim Helu da iyalansa- $89.1bn
- Larry Page- $88.9bn
- Sergey Brin- $85.2bn
- Steve Ballmer- $83.1bn
Jami’an EFCC Sun Kama Wani Manajan Banki Kan Ɓoye Sababbin Kuɗin Naira
A wani labarin na daban kuma jami’an hukumar EFCC sun cafke manajan wani banki.
Jami’an Hukumar EFCC sun kama wani manajan ayyuka na wani babban bankin kasuwanci da ke yankin tsakiyar Abuja a ranar Litinin, bisa laifin kin sanya kudi a na’urar ATM.
Wannan kamun na zuwa ne bayan manajan ya rike Naira miliyan 29 na sabbin takardun kudi na Naira a cikin bankin.