Sakamakon yunkurin sayen matashin dan wasan Gunners da kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa ta yi, Dan wasan Arsenal din ya sabun ta kwantiragin sa na cigaba da zama a kungiyar.
Emile Smith Rowe ya Sanya wa Arsenal hannu a gwantaragin shekaru masu yawa, inda kuma nan take kungiyar ta Arsenal ta saka mishi da rigar Lamba Goma na kungiyar.
Matashin Dan wasan na Gunners ya kasance abun bukatar kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa a wannan kakar, inda kungiyar ta mika wa Arsenal tayin dauwasan har sau biyu, Amma Gunners ta ki amince wa da cinikin saida matashin dan wasan.
Kazalika sanya hannun a kwantiragin na nuna cewa, Smith Rowe ya kawo karshen rade-raden tashin shi a kungiyar, inda ya kwashe shekaru sama da goma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Madrid na Son sayarwa da Chelsea Hazard
Smith Rowe ya sanya hannu a sabon kwantiragin shekaru 5 a kungiyar ta Arsenal, Wanda hakan zai sa ya cigaba da zama a Arsenal har nan da shekarar 2026.
Dan wasan tsakiyar wato Smith Rowe ya fafata wa kungiyar a wasannin 33 a kakar wasan da ta gabata, inda ya gefa kwallaye 4, kuma ya cima kungiyar kwallo a wasan share fage da kungiyar Arsenal din tasha kashi da ci 2:1 a hannun kungiyar kwallon kafa ta Hibernian.