Gabanin da ake sa ran fara kakar wasan kwallon kafa ta 2021/2022, masu rike kambun gasar Firimiyar gida Najeriya sau bakwai, Rangers International sun tabbatar da daukar sabbin ‘yan wasa 13 har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na kungiyar Norbert Okolie ya fitar, kungiyar ta samu nasarar daukan tsohon dan wasan baya na kungiyar Sunshine Stars FC, Oluwaseun Olulayo da tsohon dan wasan kasa Nigeria a gasar U-17, Okoh Chizoba.
Idan dai za a iya tunawa a kwanakin baya Rangers ta samu dauko Ossy Martins, Bamidele Adeniyi, Eboko Ikechukwu, Julius Ikechukwu, Samuel Pam, Philip Clement, Bala Akintunde, Obiorah Emeka, Olawale Doyeni, Ejike Uzoenyi, David Chimezie, da kuma wadanda za su hada kai da ’yan wasan kulob din da suka ci gaba da kalubalantar samun karramawa a kakar wasa mai zuwa.

KARANTA WANNAN LABARIN: Ɗan Shekaru 25 Suleiman Mohammed ya zama Shugaban Matasan Jam’iyyar PDP na Ƙasa
An kammala cinikin ‘yan wasan biyu ne a ranar Juma’a, 29 ga Oktoban shekarar, 2021, bayan da ‘yan wasan, masu shiga tsakani, da shugabannin kulab din suka amince da kwantiragi ln Yan wasan.
Olulayo ya ce “Yana da kyau na gwada basirar da Allah ya ba ni zuwa wani sabon gida a Enugu inda nake fatan bayar da duk abin da na yi don taimakawa kungiyar ta cimma burinta na kakar wasa mai zuwa.”
Okoh, wanda ya kasance a sansanin ‘yan kasa na Yan kasa da shekaru 17 a shekarar 2019 yana dan shekara 16 ya samu kwangilar sa ta farko tare da kungiyar River-Lane Youth Academy, dake garin Enugu.
Comments 1