Kungiyar Magoya bayan Kwallon kafa a Burtaniya sun zabi Mohamed Salah a matsayin gwarzon dan wasan kwallon kafa na shekara a kasar.
Dan wasan gaba na Liverpool ya sake lashe kyautar a karo na biyu, bayan kuma an ba shi kyautar a shekarar 2018. Ya zama dan wasa na farko a tarihin kyautar da ya lashe kyautar fiye da sau daya.
Masoyan kwallon kafa na dukkan kungiyoyi ne suka zabi Salah domin ya doke Mason Mount da Michail Antonio da Phil Foden da Ruben Dias da kuma Youri Tielemans a kyautar.
Dan kasar Masar ya fara kakar wasa ta 2021-22 cikin yanayi mai ban mamaki, inda ya zura kwallaye 17 a wasanni 18 da ya bugawa kungiyar Liverpool.