Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta doke Crystal Palace da ci 2 da nema a wasan farko na gasar Firimiyar Ingila a kakar 2022/2023.
Fafatawar dai ta gudana ne a filin wasa na Selhurst Park a ranar Juma’ar nan.
Anthony Taylor shine ya jagorancin alkacin wasan da kungiyoyi biyun suka kai ruwa rana.
Dan wasa Gabriel Martinelli shine ya Fara zura kwallon farko a minti na 20 bayan samun tai mako daga sabon dan wasan Arsenal Oleksandr Zinchenko.
Sai Kuma kwallo ta biyu da dan wasa Marc Guehi ya zura a ragar kungiyarsa wato Own goal.
A kalla dubban magoya baya ne dai suka halarci kallon wasan da shine na farko na kakar shekarar 2022/2023 da aka fara.