Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya yi imanin cewa rashin nasarar da kungiyarsa ta yi a wasanninta da Liverpool da West Ham United a kakar wasa ta bana ta yi tsada a fafatawar neman lashe gasar Premier,Daily Post ta rawaito.
Arteta ya yi wannan maganar ne bayan wasan gasar Premier da Arsenal ta doke Nottingham Forest 1-0 ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin Da Yasa Arsenal Ta Barar Da Damar Lashe Gasar Premier — Arteta Yayi Bayani Dalla-Dalla
Sakamakon wasan da suka buga da Forest na nufin Manchester City a yanzu ta zama zakara a Ingila wanda ya rage mata saura wasanni uku ta buga.
Da yake magana da manema labarai game da kungiyoyin da watakila sun baiwa Arsenal damar lashe gasar bana, Arteta ya ce bayan wasan da suka yi da Forest, “Ya fara ne da abin da ya faru a Anfield [da Liverpool] a cikin minti na 90. Sannan a West Ham, yace idan kun ajiye shi don yin 3-1 komai ya canza.”
Ya kara da cewa, “An zura mana kwallaye da dama. Mun ba da kwallaye 16 a waje a wadannan wasannin. Kaddara ce.
“Ba za ku iya kiyaye hakan ba. A cikin wannan gasar, dole ne ku kasance na musamman tare da komai saboda babu tabo.
“Wannan tawagar ba ta ba ku wani tabo ba. Mun tsawaitawa wannan tazarar da yawa, kuma shi ya sa muka yi rashin nasara a gasar.”
Ku tuna cewa Arsenal ta sunyi watsi da ci 2-0 inda suka tashi 2-2 tsakaninta da Liverpool da West Ham United a watan Afrilu.
A wani labarin kuma, UCL: Abin Da Guardiola Ya Gaya Mani Kafin Wasan City da Madrid – Rio Ferdinand
Tsohon dan wasan kasar Ingila, Rio Ferdinand ya ce kocin Manchester City, Pep Guardiola ya shaida masa cewa kungiyarsa za ta doke Real Madrid a wasan kusa da na karshe.
Guardiola ya shaida mani cewa kungiyarsa za ta doke Spain kamar yadda suka yi shekaru biyu da suka gabata.