Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester United taci wasanta na farko a gasar Firimiyar Ingila, yayin da ta kara da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool.
Jaridar ALKIBLAH ta rawaito cewa wasan da aka fafata shi a Old Trafford an tashi ne da ci 2 da 1.
KARANTA ANAN: Akwai Yiwuwar Samun Ɓaraka Kan Shirin Daukar Sabbin Jami’an Ƴan Sanda
Yan wasa Jadon Sancho da Marcus Rashford ne suka ci kwallayen biyu, wanda suka baiwa Man United din nasara.
Dan wasa Muhammad Salah shima yayi rawar gani a wasan da suka buga a yau tun a mintuna na 9 da take wasan.
A wani labarin kuma: Magoya Bayan Peter Obi Barazanar PDP da APC Ne – Fani Kayode
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya ce magoya bayan Peter Obi hadari ne ga jam’iyyun PDP da APC.
Mabiyan dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar Labour Party ana kiransu da ”Yan gani kashe ni” “Obidients”.
A cikin wata makala tasa, Fani-Kayode ya ce yana da sha’awar sanin wanda suke marawa baya, da kuma wadanda suke wakilta.