Mahukunta sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan din nan Christian Eriksen na nan da ransa bai mutu ba.
Dan wasan ya yanki jiki ya faɗi ne a karawar kasarsa ta Denmark da Finland a ranar Asabar cikin gasar Euro 2020.
An baiwa dan wasan mai shekara 29 agajin gaggawa tun a tsakiyar fili, gabannin daukarsa ranga-ranga zuwa asibiti.
To sai dai wata sanarwa da hukumomi suka fitar a ranar Lahadi ta ce dan wasan yana can yana ci gaba da karɓar kulawar lafiya, kuma babu wata bukatar tada hankali dangane da yanayin lafiyarsa.
“Mun yi magana da Christian Eriksen da safiyar nan, kuma har gaisa da abokan wasansa”
Da ma dai lamarin ya faru yayin da aka jefa wa ɗan wasan ƙwallo, amma kafin ya kai garesa sai ya yanki jiki ya faɗi.