Daga Sulaiman Umar AC
Akwai Yiyuwar Everton ta doke Arsenal wajen daukar dan wasan baya na Getafe me suna Djene Dakonam dan shekaru 27 da kungiyar tace dole a biya ta fam miliyan 30 akansa.
Dakonam na daya daga cikin taurarin kungiyar ta Getafe wacce ta bawa kowa mamaki wajen kare gasar Laliga ta bana a mataki na 5.
Sai dai kuma kasancewar Arsenal tayi kasafin kudin fam miliyan 45 ne kawai na sayen `yan wasa a wannan kasuwar `yan wasannin yasa dole Unai Emery ya maida hankalinsa ka `yan wasa masu saukin kudi ba irinsu Dokanam da yake da kudi fam miliyan 30 ba.
Shi kuwa a nasa bangaren mai koyarwar Everton Marco Silva yana kallon dan wasan Dokanam a matsayin wanda zai maye masa gurbin dan wasa Zouma wanda zamansa na aro a kungiyar zaizo a karshe a wannan wata