Everton na kokarin shawo kan Wayne Rooney ya maye gurbin Frank Lampard a matsayin kocinta.
An kori Lampard ranar Litinin tare da Toffees a cikin mummunan yanayi, wanda fuskar kowa babu dadi.
KU KARANTA: Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gaggauta Kawo Karshen Yajin Aikin Ma’aikatan NAHCO
Jaridar Goal ta ruwaito cewa kungiyar ta Premier ta tuntubi Rooney a zahiri, domin tana ganin zata iya cika fatan da take da shi akan halin da suke ciki yanzu haka.
A halin yanzu dai Rooney ne ke jagorantar kungiyar DC United a gasar MLS, amma yana da kwarin guiwar komawa Ingila da karbar ragamar horar da kungiyar a Goodison Park.
A baya dai tsohon dan wasan na Manchester United ya bayyana kin amincewa da damar kocin Everton a watan Janairun 2022 kafin a nada Lampard.
A wani labarin kuma: Ka Shirya Takaddun Mika Mulki — APC Ta Yi wa Gwamnan PDP Mai Ci Barazana
Jam’iyyar APC ta bukaci gwamnan jihar Bauchi mai ci, Bala Mohammed, da ya fara shirya takardun mika mulki. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na kasa, Yakubu Murtala-Ajaka, wanda ya bayyana hakan a yayin taron kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar a jihar Bauchi a ranar Litinin, ya ce jam’iyyar APC ta tanadi duk wata hanyar dimokuradiyya domin kawar da gwamnan da ke zama dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP.
Ajaka ya bayyana kwarin guiwar cewa dan takarar jam’iyyar APC kuma tsohon shugaban hafsan sojin sama, Sadique Abubakar ne zai lashe zaben da za a yi a ranar 11 ga watan Maris, ya kuma kafa sabuwar Gwamnati a Bauchi.