Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta tayar da kura kan wani shafin LinkedIn da ake zargin na magatakardata Farfesa Is-haq Oloyede ne.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta JAMB, Dr Fabian Benjamin ya fitar, ya ce shafin na bogi ya dade yana aikewa da jama’a bukatar abokantaka.
Ya bayyana irin wannan makirci da aka fara da nufin damfarar jama’a wanda ba su da tushe balle makama.
KARANTA HAKANAN Hukumar ICPC Ta Sake Damke Magatakardan Hukumar JAMB
Sanarwar ta kara da cewa “Hukumar tana son bayyana cewa Farfesa Is-haq Oloyede ba shi da mallaka ko sarrafa duk wani shafin sada zumunta kuma bai nemi wani ya bude ko sarrafa daya a madadin sa ba.”
Yayin da aka lura cewa LinkedIn shafin yanar gizon zamantakewa ne wanda aka tsara musamman don ‘yan kasuwa. Don haka, ya kamata a lura cewa burin shafin shine don baiwa masu amfani da rajista damar yin hulɗa tare da mutanen da suka sani kuma suka amince da su a sana’a, in ji shi, Farfesa Oloyede ba ya cikin wannan rukuni na mutane kuma ba ya nufin shiga.
Ya ce wannan furucin ya zama dole duba da wasu marasa kishin kasa, wadanda aka ce sun bude shafin LinkedIn a madadinsa domin damfarar wasu jama’a da ba su ji ba gani ba, da ikirarin bogi na malamin nan na bogi na taimaka wa harkokin kasuwanci na sadarwa, gudanar da sana’o’i, samar da ayyukan yi gudanar da kamfanin bincike ko haɗa mutane tare da abokan hulɗar kasuwanci na kamfanoni ko masana’antu ta hanyar asusun.
Hukumar, duk da haka. ya bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan da wadannan miyagun abubuwa domin kada su fada hannun ‘yan damfara.
A Wani Labarin Kuma Bashin N18.7Bn: Majalisar Dokokin Kebbi Ta Yi Sammaci Gwamna Bagudu
Majalisar dokokin jihar Kebbi ta gayyaci gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu kan bayanin yadda ya yi amfani da bashin Naira biliyan 18.7 daga gwamnatin tarayya.
A cikin wasikar da majalisar ta aike wa gwamnan mai kwanan wata 26 ga watan Janairun 2023, majalisar ta bukaci gwamnan ya bayyana a gabanta a ranar Juma’a 27 ga watan Janairun2023.