By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane uku ne aka hallaka tare da jikkata wasu da dama a ranar Lahadi a karamar hukumar Offa da ke jihar Kwara yayin da wasu samari suka yi arangama bayan da aka samu rashin jituwa kan wata budurwa.
An tattaro cewa lamarin ya fara ne a daren ranar Asabar lokacin da rikicin ya barke tsakanin masoyan budurwar.
Jami’an Ƴan Sanda Suyi Ram Da Wasu Mutane Biyu Dauke Da Kan Bil’adama A Jihar Kwara
Wani mazaunin garin mai suna Alhaji Abdulrahman ya shaida wa manema labarai cewa rikicin ya faru ne tsakanin samarin Isale Oja da Oja Oba a garin Offa.
A cewarsa, daya daga cikin shugabannin kungiyar an ce ya sace budurwar daya ban garen kungiyar da ya kai ga barkewar fada.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da mutuwar ‘yan dabar guda biyu, inda ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
“Kafin isowar ‘yan sanda an harbe biyu daga cikin ‘yan kungiyoyin da suka hadar da Samad Adeyemi mai shekaru 21 da kuma Abdulahi Mohammed mai shekaru 20 har lahira.
“Duk da haka ana ci gaba da bincike kan lamarin,” in ji shi a cikin wata sanarwa.
Comments 1