Kotu ta dakatar da shirin gwamna Obaseki na jihar Edo kama Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole da yake shirin yi. Wata kotun koli dake zamanta a Abuja ta dakatar da gwamnan Edo Godwin Obaseki da nufin kama shugaban jam’iyyar APC bayan da ya shigar kokensa gaban kotu.
A watan Janairu ne gwamna Obaseki ya kafa wani kwamitin bincike aka wani asibitin kwararru da tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole ya gina.
A watan Mayu kuwa, kwamitin sun kammala bincikensu tare da gabatar da binciken ga gwamna Obaseki, inda suka ce sun gano Oshiomhole yayi almundahana da kudin gwamnati tare da saba doka wajen fitar da kudin aikin.
Kwamitin sun shawarci da gwamnatin jihar da ta kama tsohon gwamnan domin yi masa hukunci. https://dimokuradiyya.com.ng/saurin-fushi-kotu-ta-yankewa-wani-hukuncin-kisa-sakamakon-kashe-mahaifinsa/
Daga bangarensa kuwa, Oshiomhole ya shigar da kara kotu ta hannun lauyansa West Idahosa, inda ya roki kotun da ta dakatar shirin kama sa da kwamitin ke yi.
Daga bangarensa kuwa lauyan gwamnati Alex Ejeiseme, yayi watsi da hukuncin da kotun ta yanke inda yace tabbas Oshiomhole na bukatar a masa hukunci.
Daga cikin wanda suka halarci zaman kotun akwai Alkalin alkalai na jihar Yinka Omorogbe, mai shari’a James Oyomire, shugaban hukumar ‘yan sanda na jihar, tare da shugaban hukumar farin kaya ta jihar.
Mai Shari’a Ahmad Mohammed ya dake zaman kotun zuwa 17 ga watan da muke ciki.