Dubban al’ummar Hausawan Sudan ne suka kafa shingaye tare da kai hari kan gine-ginen gwamnati a garuruwa da dama a ranar Litinin din nan , kamar yadda shaidu suka bayyana, bayan shafe mako guda ana kazamin fadan kabilanci a kudancin kasar.
A wani yunkuri na yin karin haske kan rikicin da ya barke a jihar Blue Nile, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 60 tare da raunata wasu 163 a cewar hukumomin yankin, masu fafutuka na Hausa sun gudanar da zanga-zanga yau ranar Talata a birnin Khartoum na kasar Sudan.
Rikicin, tsakanin kabilar Berti da Hausawa, ya fara barke ne a ranar Litinin din da ta gabata, bayan da ‘yan kabilar Bertis suka ki amincewa da bukatar Hausawa na samar da “Hukumar farar hula da za ta sa ido kan yadda ake samun filaye”, kamar yadda wani fitaccen dan Hausa ya shaida wa Kamfanin dillancin Labarai na AFP da ya nemi a sakaya sunansa.
Sai dai wani jigo a kabilar Bertis ya ce kabilar na mayar da martani ne ga wani “cin zarafi” da Hausawa suka yi musu.
Gwamnan Blue Nile Ahmed al-Omda a ranar Juma’a ya haramta tarukan jama’a da gudanar da zanga-zanga na tsawon wata guda tare da sanya dokar hana fita na dare a jihar da ke kan iyaka da Habasha.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce hukumomi za su “dauki mataki” a kan masu tayar da “wariyar launin fata, ƙiyayya da kuma rikici,” a cewar kamfanin dillancin labarai na SUNA.
A ranar Asabar ne aka jibge sojoji a kogin Blue Nile, kuma tun daga lokacin aka samu kwanciyar hankali a can ko da yake an sake samun tashin hankali a wasu wurare.
A birnin Kassala da ke gabashin kasar, gwamnati ta hana tarukan jama’a bayan da dubban Hausawa “sun bankawa gine-gine da shaguna na gwamnati wuta”, a cewar wani ganau Hussein Saleh.
“Abin tsoro ne a tsakiyar birnin,” wani mazaunin Kassala Idriss Hussein ya shaida wa AFP ta wayar tarho. Ya ce masu zanga-zangar suna ” toshe hanyoyi suna daga sanduna.”
A birnin Wad Madani mai tazarar kilomita 200 (kimanin mil 125) kudu da birnin Khartoum, “daruruwan al’ummar Hausawa ne suka kafa shingaye na duwatsu tare da kona tayoyi a kan babbar gada don hana zirga-zirga,” kamar yadda wani mazaunin garin Adel Ahmed ya shaida wa AFP.
Masana sun ce juyin mulkin da sojoji suka yi karkashin jagorancin Hafsan Sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan a watan Oktoban shekarar 2021 ya haifar da tabarbarewar tsaro da ya haifar da sake barkewa a rikicin kabilanci, a kasar da ake fama da munanan tashe-tashen hankula a kai a kai kan filaye, dabbobi, samun ruwa da kiwo.
Masu rajin kare demokradiyya sun zargi sojojin Sudan da tsaffin shugabannin ‘yan tawayen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta 2020 da ta’azzara rikicin kabilanci a kogin Blue Nile don cimma wata manufa ta kashin kai.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa Hausawa dai na daya daga cikin manyan kabilu a nahiyar Afirka, inda miliyoyin mambobi ke zaune a kasashe da dama.
Akwai Hausawa miliyan uku a kasar Sudan, inda galibinsu mabiya addinin Musulunci ne, amma suna jin yarensu na asali maimakon Larabci.
Yawancinsu suna rayuwa ne ta hanyar noma a yankin Darfur, jihar Al-Jazira da kuma jahohin Kassala da ke gabacin Gedaref da Sennar da Blue Nile.
-AFP