Wani mai auren mata fiye da daya a jihar Enugu, Cif Simon Odo, wanda aka fi sani da ‘Dan Shaidan’ ya rasu yana da shekaru 74 a duniya.
Cif Simon Odo ya auri mata 59 kuma yana da ‘ya’ya da jikoki sama da 300 kafin rasuwarsa.
Wani faifan bidiyo da jaridar DAILY POST ta samu a safiyar Laraba ya nuna cewa an yi jana’izar marigayin.
Emeka Odo, daya daga cikin ‘ya’yansa ne ya bayyana wa manema labarai rahoton rasuwar mahaifin nasa a ranar Talata.
Emeka ya shaida wa manema labarai cewa Odo, wanda likitan ne dan asalin Aji a karamar hukumar Igbo-Eze ta Arewa a jihar Enugu, kafin rasuwarsa, ya yi gargadin cewa kada a kai gawarsa dakin ajiye gawa.
Ya ce: “Ya shafe kusan makonni uku yana fama da rashin lafiya. Muna yin taron dangi don yin cikakken shiri don binne shi yayin da ya ba da umurni cewa kada mu saka shi a dakin ajiyar gawa.”
Faifan Bidiyon Yadda Aka Burne Mai Mata 59, Da Yaya Sama Da 300, Tare Da Motarsa A Enugu
Wani mai auren mata fiye da daya a jihar Enugu, Cif Simon Odo, wanda aka fi sani da ‘Dan Shaidan’ ya rasu yana da shekaru 74 a duniya.
Cif Simon Odo ya auri mata 59 kuma yana da ‘ya’ya da jikoki sama da 300 kafin rasuwarsa.
Wani faifan bidiyo da jaridar DAILY POST ta samu a safiyar Laraba ya nuna cewa an yi jana’izar marigayin..