Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya bayyana damuwarsa dangane da abinda jam’iyyar APC zata gayawa yan Najeriya, dangane da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa.
Gwamnan na wannan batu ne a yau, lokacin da yake ganawa da manema labaran fadar shugaban kasa, bayan da ya gana da shugaban kasa Muhammad Buhari a fadarsa dake Villa.
Kazalika ya kuma bayyana maimakinsa, kan yadda APC ke ganin cewa ta yi ficen da har Goodluck zai iya tsayawa takara a cikinta, kuma kujerar lamba daya.
A don haka ne ya ce abu ne mai matukar wahala ga APC ta kai bantenta, ta hanyar amfani da sunan Goodluck a matsayin dan takarar shugaban kasa.
”Sannan kuma sanya shi cikin masu son zama shugaban ƙasa shima abun kunya ne ga duniya ba iya Najeriya ba.” inji Shi.
Tuni dai Goodluck Jonathan ya raba gardama inda ya nesanta kansa da komawa jami’iyyar APC don yi musu takara.