By Abbas Yakubu Yaura
Mutane da dama ne suka jikkata sakamakon wani sabon rikici da ya barke tsakanin Falasdinawa da jami’an tsaron Isra’ila a kan Dutsen Temple da ke tsohon birnin Kudus, wanda musulmi ke kira da Wuri Mai Tsarki.
Kamfanin dillancin labarai na Falasdinawa ya rawaito daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, tashin hankalin da aka yi a ranar Juma’ar karshe ta azumin watan Ramadana, ya yi sanadin jikkatar mutane kimanin 42.
Mutane Biyu Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata A Wani Hatsarin Motar Bas A Jihar Legas
Rahoton ya ce an yi ta arangama da juna a kan Dutsen Temple cikin makonni biyun da suka gabata, yayin da al’amuran tsaro a duk fadin Isra’ila ke ci gaba da tabarbarewa bayan hare-haren da aka kai.
A cewar ‘yan sandan, daruruwan mutane ne, wasunsu rufe da fuska, suka tada tarzoma a wurin mai tsarki.
Rundunar ‘yan sandan ta ce an yi jifa da duwatsu da kuma wasan wuta a kan katangar Yamma, wurin da Yahudawa ke taruwa don yin addu’a, daga nan ne suka shiga yankin domin kwantar da tarzoma.
Filin Dutsen Temple shine wurin Dome na dutsin Masallacin al-Aqsa, wuri na uku mafi tsarki a Musulunci.
Hakanan yana da tsarki ga Yahudawa domin haikalin Yahudawa biyu suna tsaye a wurin.
Filin yana karkashin kulawar musulmi ne, yayin da Isra’ila ke da alhakin samar da tsaro.
Bisa yarjejeniyar da aka yi da hukumomin musulmi, an yarda Yahudawa su ziyarci wurin amma kada su yi salla a wurin.
Falasdinawa dai na zargin Isra’ila da kokarin fadada ayyukan yahudawa ‘yan kamaguri zauna masu sa ido a wurin mai tsarki.
NAN
Comments 2