Tsohon Ministan Harkokin wasanni Solomon Dalung yace karbar Femi Fani-Kayode a Jami’iyyar APC, abune wanda hankali bazai dauka ba.
Ya bayyana Fani-Kayode a matsayin mai siyasar talla, kuma marar amfani da a Jami’iyyar.
A jawabin daya fitar a ranar Juma’a, Dalung yace yana jin kunya yadda Buhari ya zauna teburi daya da wanda ya kirashi ‘Dan ta’adda’.
Daga cikin jawabin da Dalung ya fitar yace “a dukkanin rayuwa ta, ban taba jin kunyar kaina ba irin ranar Alhamis, a lokacin da na kalli Femi Fani-Kayode na tsaye, tare da Shugaban Kasa a Villa Abuja. Banda matsala da bambancin siyasa a tsakanin mutane, amma Ina jin babu dadi na yadda ake wasa da mutuncin Yan Nigeria daga Shuwagabannin siyasa, kamar yadda majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kashe Shugaban Miyetti Allah, a wani sabon hari da suka kai a Kaduna
“Shin karbar Yan siyasa marassa amfani a madadin matsalar tsaro daya addabi rayuwar yan Nigeria da suka yi zabe yafi a yanzu?
“Abunda ya faru ga Shuwagabannin Jami’iyyar APC ya nuna cewa akwai son kai, idan muka dauki dabi’ar dawo da abokanan hamayya kamar su Femi Fani-Kayode, amma muka fadi Kasa warwas wajen magance Yan Boko Haram da yan bindiga dadi da Yan ta’adda gami da masu garkuwa da mutane to minene amfanin haka?”
Ya bayyana bakin cikinsa na yadda muradun da Jami’iyyar APC ta sanya a Shekarar 2015 wanda ya sanya aka zabe ta, ya canja, yana mai bayyana cewa mutane na shiga Jami’iyyar domin samun mukamai masu armashi.
Dalung yace “wannan ba shine muradun mu ba a lokacin da muka nemi Yan Nigeria su amince damu a Shekarar 2015. Jin tsoron Jami’iyyar APC shine baiwa, domin da zaran ka shiga Jami’iyyar shikenan an yafe maka zunubbanka dukkanin su, duk wata kara ta cin hanci yanzu za’a ajiye ta, tare da biyan diyya da mukamai masu girma.
“Biyayya a Jami’iyyar shine babban laifi, babu mamaki Femi Fani-Kayode ya zagi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kuma Sowore ya kwammace ya mutu da ya shiga Jami’iyyar APC.
“Yanzu ya zama shalelen Dan siyasar Shugaban Kasa, Wanda ya kira Dan ta’adda’. Idan wannan ne Jami’iyyar zata iya badawa a wannan hali na matsatsi na tarihin Nigeria, to gaskiya Nigeria ta shiga wani hali.”
Comments 1