Faransa ta bukaci a gudanar da cikakken bincike kan rahotannin da ke cewa dakarun gwamnati da sojojin haya na Rasha sun kashe daruruwan fararen hula a Mali.
Kungiyar tarayyar Turai wato EU da kuma kasar Amurka sun yi irin wannan kiraye-kirayen da suka shafi mace-mace a yankin tsakiyar garin Moura.
A ranar Juma’ar da ta gabata ce rundunar sojin kasar ta Mali ta ce ta kashe mayakan Islama fiye da 200 a cikin kwanaki 10 da aka kwashe ana gwabza fada a yankin.
Har yanzu dai ba a iya tantance ko su waye aka kashe ba, a yayin fafatawar
Sai dai Kasar Mali ta musanta cewa sojojin hayar kungiyar Wagner ta kasar Rasha suna taimaka mata wajen yakar masu tsats-tsaurar ra’ayin addinin Islama.
Comments 1